Yayi rantsuwa
JARIDAR HAUSA:Wani saurayi ya yankewa kan shi wani mugun hukunci bayan da soyayya ta rude shi ya rantse da Al'kura'ni Mai girma cewar ba zai taba kula wata Mace ba sai wannan budurwar tasa.
Hakan ya faru ne bayan da Budurwar tasa ta tsare shi a cikin Motar sa lokacin daya zo wajen ta zance.
Tayi amfani da wannan damar ta bashi Al'kura'ni Juzu'i Sitti ya dafa tare da yin Alkawarin duk ranar daya kula wata Mace ba ita ba Alkur'ani ya ci shi.
Matashin ya sha suka bayan bayyanar sabon Faifayin Bidiyon a sabbin kafafen sadarwa na Zamani, wadansu harda tsinuwa.
Sau tari Soyayya takan rudi Mutun karshe ma yazo yayi aikin dana sanin, anya babu ganganci kan saurayi ya rantse da Alkur'ani cewar ba zai taba kula wata Mace ba sai Budurwar sa kadai?
Ku kalli cikaken Bidiyon.
Comments
Post a Comment